Sanatocin APC sun ki yarda a sauya ranakun zabe

0

Wasu gungun Mambobin Majalisar Dattawa su goma, sun bijire wa rahoton kwamitin majalisar kan sauya ranakun zaben 2019 da INEC da gindaya tun da farko.

Musammam, wadannan sanatoci sun ki yarda a yi wa dokar sashe na 25 kwaskwarima, wadda ita ce dokar da ta bayyana ranakun da za a yi kowane zabe.

Majalisar Tarayya ce ta fara yi wa sashen dokar gyara, inda ta maida cewa sai dai a fara yin zaben Majalisar Tarayya kafin na majalisar jihohi da na gwamnoni, sannan a yi na shugaban kasa daga karshe.

Wadannan sanatoci 10 sun fice daga zauren majalisa dattawa a fusace, suka kira taron manema labarai, inda nan take su ka bayyana cewa duk wani shiri na sauya ranakun zabe, haramtacce ne, ba za su amaince da shi ba,

Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nassarawa shi ne jagoran sanatocin wadanda suka yi tawaye.

Ya ce ba su kadai ba ne su ka ki yarda da sauya ranakun, domin hatta shugaban kwamitin sauya ranakun da sakataren sa ma ba su sa hannun amincewa ba.

Ya ce shirin wata kullalliya ce da ake harin wani mutum daya da mugun nufi. Kuma ba za su amince da hakan ba.

Wani sanatan kuma ya ce su kan su mambobin majalisar tarayya da suka zartas da sauya ranakun zaben, yawan su bai kai yawan adadin da ya kamata a ce su ne doka ta amince su sauya ranakun ba.

Sanata Umaru Kurfi, daga jihar Katsina, ya ce maganar ranakun da za a gudanar da zabe batu ne da ya shafi hukumar zabe, ita ce doka ta ba ta ikon yin sha’anin ta. Don haka babu ruwan majalisar dattawa ko ta tarayya da yin shiga-sharo-ba-shanu.

Share.

game da Author