Sanata ya nemi Buhari ya hana gwamnoni tururuwa zuwa fadar sa

0

Sanata Shehu Sani ya yi Allah-wadai da halayyar gwamnonin kasar nan da su ke yawan barin nauyin da aka dora musu, maimakon su tsaya jihohin su suna yin aiki, sai kullum su na fadar shugaba Muhammadu Buhari.

Sani, wanda shi ne sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya ce a lokacin da jihohin wadannan gwamnonin ke cikin rikice-rikice, su kuma gwamnonin su na Abuja kullum su na fadanci da Fadar Shugaban Kasa.

A kan haka ne sanatan ya nemi Buhari ya taka musu burki haka nan, ya ce wannan ziyara ta ba gaira ba dalili, ta isa haka nan.

Sani ya yi wannan jawabin ne ranar Asabar, biyo bayan yadda wasu jihohi ke fama da rikici alhali gwamnonin jihohin su na fadar shugaban kasa, sun wofintar da al’ummar da ke kan su.

Gwamnan Zamfara. Abdul’aziz Yari na daga daga cikin gwamnonin da ke fuskantar wannan caccaka, ganin yadda ya na kwance Abuja mahara su ke kashe-kashe a jihar sa, ba shi da labari, kuma bai kai daukin gaggawa ba.

Sani ya ce banda siyasa da bambadanci babu abin da ke kai gwamnonin Fadar Shugaban Kasa, da nufin su rika nuna masa wai su su na goyon bayan sa, alhali kuma sun baro jama’ar jihohin su a hannun talasurun mataimakan gwamnoni da kuma makasan da sai cin karen su babu babbaka su ke yi.

Har ila yau, Shehu Sani ya nuna bacin rai yadda manyan Arewa suka yi shiru, basu fitowa suna fada wa shugaban kasa gaskiyar lamarin yadda kashe-kashe ya kazamce a yankin Arewa.

Share.

game da Author