Sanata Abubakar Kyari na jihar Barno ya ce ba gaskiya ba ne da hukumar sojoji su ka ce an kakkabe Boko Haram kwata-kwata.
Kyari ya ce har yanzu ba a gama kwato karamar hukumar Marte, daya daga cikin kananan hukumomin da ya ke wakilta daga hannun Boko Haram ba.
Ya ce shi ne kadai wakilin da ya rage wanda wani yanki da ya ke wakilta ke karshin Boko Haram, har yanzu jama’ar sa ke a tarwatse.
Sanatan na Barno ta Arewa, ya na wakiltar kananan hukumomi 9 ne.
“Cikin 2015, gaba dayan kananan humumomin da na ke wakilta duk a tarwatse suke in banda karamar hukumar Gubio da wasu guda biyu. Kuma kada a manta, ni ne fa sanatan da aka zaba da kuri’un da ka kada a sansanonin’yan gudun hijira.”
Ya ce har yau Arewacin karamar hukumar Marte a tarwatse ta ke. Na farko dai ga Boko Haram na yawan kai hare-hare, su kuma sojoji a yankin sun a tsaurara tsaron da bai ma yiwuwa jama’a su iya samun walwalar yin harkokin kasuwanci ko kananan sana’o’i.
Kyari ya yi wannan martini ne ga jawabin da Ministan Tsaro, Mansir Dan’ali ya yi a wurin taron da aka yi a Maiduguri, inda ministan ya ce an kakkabe Boko Haram dungurugun.