Tsohon ministan wasanni Samaila Sambawa ya canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Da yake karbar Sambawa da dandazon magoya bayan sa sama da 100,000 a filin wasa dake Birnin Kebbi gwamnan jihar Abubakar Bagudu, ya ce jam’iyyar APC na farin cikin da wannan kamu da tayi sannan yayi kira ga sauran ‘yan PDP da su bi sahun Sambawa a jihar.
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Attahiru Maccido, ya jinjina wa Sambawa da magoya bayan sa sannan yayi masu lale marhaba da shigowa jam’iyyar APC.
Da yake na sa bayanin, Sambawa ya ce ya yanke wannan shawara ne ganin irin dimbin ci gaba da aka samu a karkashin gwamnatin jihar da kasa baki daya.
Ya bayyana cewa bayan bunkasa da aka samu a fannin noma musamman a Jihar, wutan lantarki ya inganta sannan tsaro da ci gaban kasa ya yalwata.