Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ware naira miliyan 65 a cikin 2017, wadda yace ya kashe kudin ne wajen bude shafin intanet.
Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin bin diddigin da PREMIUM TIMES ta yi wa kasafin kudin 2017, na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, inda ta ci karo da wannan bayani cewa an kashe naira milyan 65, 855,875 wajen aikin bude shafin intanet na ofishin.
Binciken ya kuma ga wurin da aka rubuta cewa gaba dayan kudin sun shige a wurin aikin ba a samu rarar ko kwandala ba.
A yanzu dai Bode Mustapha shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda shi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada cikin watan Oktoba, 2017, bayan cire Babachir Lawal. An dai samu Lawal da laifin harkallar naira milyan 250 ta aikin kwangilar guntule ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira.
Sai kuma duk da wannan bincike da PREMIUM TIMES ta bankado, ba ta gano ko a karkashin wane shugaban ba ne tsakanin Lawal da Mustapha ya bude shafin intanet daya tal da naira milyan 65 ba.
Da PREMIUM TIMES ta tambayi kakakin yada labaran Sakataren Gwamnati, Mohammed Nakorji, sai ya ce ba zai iya cewa komai ba, domin shi babu abin da ya hada shi da aikin akawu, ballantana ya san yadda aka kashe kudaden dalla-dalla.
Discussion about this post