Sai da aka ci zabe aka maida miji na saniyar-ware – Remi Tinubu

0

Uwargidan Sanata Bola Tinubu, wato Sanata Remi Tinubu, ta bayyana cewa ta sha gaigaya masa don me ya ke zakalkalewa wajen nuna goyon bayan gwamnatin APC, duk da irin wulakanta shi da ta yi?

Remi ta ce gwamnatin APC ta wulakanta mijin ta, duk kuwa da rawar da ya taka wajen kafa gwamnatin, amma jim kadan da kafa mulki, sai aka rika kaffa-kaffa da shi, aka maida shi saniyar-ware.

“Wato abin da aka yi wa miji na da ciwo sosai, ya bakanta min rai matuka. Sau da yawa na kan dube shi na ce ‘to kai ma don me har yanzu ka ke ta rabe da su? Ka watsar da su mana!”

Haka Remi ta shaida wa gidan talbijin na TVC a cikin makon nan. Ta ci gaba da cewa amma maigidan na ta bai yi fushi ba, sai dai ya kan nuna mata cewa ai shi kishin kasar ne a gaban sa, domin ya san dajin da aka keto a baya.

Wannan bayani da ta yi, shi ne kalami na farko tabbatacce da ya nuna cewa gwamnatin APC ta ci amanar Tinubu bayan ya taimake ta ta kafa mulki a 2015.

Dama dai an dade ana yada cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta watsar da Tinubu bayan an kafa gwamnati, amma bangarorin biyu su na a musantawa.

Sai dai kuma sabani na farko ya faru ne tsakanin Buhari da Tinubu, tun farkon lokacin zaben Shugabannin Majalisar Tarayya, musamman dangane da yadda Buhari ya yi sakaci har manyan mukaman su ka fada hannun wadanda ba su APC ta so a zaba a mukaman ba.

Musamman ganin yadda Bukola Saraki ya hau shugabanci bayan ya hada kai da mambobin majalisar dattawa daga PDP, sannan kuma ya dauko dan PDP aka zabe shi mataimakin shugaban majalisa.

Wannan ya gurgunta hadin kai a APC, wanda har yanzu sakamakon wannan sakacin ba bibiyar jam’iyyar.

An kuma tabbatar da cewa a wajen nada ministoci ma ba a nemi shawarar Bola Tinubu ba, sai dai ya na ana yi amma ba da shi ba.

Duk da cewa Tinubu na musanta sabani tsakanin sa da Buhari ko gwamnatin APC, a karshe dai cikin 2016 lokacin da aka yi wani wuyar mai, sai da ya fito ya caccaki ministan man fetur, Ibe Kachikwu, ya na cewa bai san abin da ya ke yi ba, kuma shi ya haifar da wahala da kuncin da al’umma ke ciki.

Watanni shida bayan wannan kuma, Tinubu ya fito ya soki lamirin shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, ya na cewa da shi aka hada kai ake yi wa Tinubu din tadiya.

Sai kuma yayin da rikici ke ta kara dagulewa a cikin jam’iyyar APC, Tinubu bai fito fili ya soki Buhari ba, duk kuwa da ganin cewa Buhari ya kyale jam’iyyar sa sai tabarbarewa ta ke yi, bai sa baki ya sasanta ba.

A nan ne sai Remi Tinubu ta ce, “To bayan an ci zabe an haye kan mulki, an maida mijin na Bola Tinubu tamkar wata bola, wane sasanci ake so ya yi kuma?

Ta ci gaba da cewa ta na jin haushinn irin wahalhalun da su da iyalan su suka shiga wajen tabbatar da cewa APC ta kafa mulki a 2015.

A daidai lokacinn da ake ta rade-radin cewa Tinubu ba zai goya wa Buhari baya a zaben 2019 ba, ko kuma ba zai zura jikin sa sosai ba, sai kuma ga shi, Buhari ya jawo shi a jika kwanan nan, inda ya nada shi a matsayin gogarman da zai sasanta rashin jituwa, sabani da rikice-rikicen da ya dabaibaye APC.

Share.

game da Author