SABUWAR RIKICI: An sake kai hari a wasu Kauyukan Kajuru

0

Wasu matasa sun kai wa mazauna kauyen Kalla hari da yake kilo mita 7 daga Kasuwar Magani a karamar hukumar Kajuru jihar Kaduna.

Mazauna kauyen sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an kai harin ne da misalin karfe biyar na yammacin Talata bayan kungiyar ‘Peace Revival and Reconciliation Foundation of Nigeria’ ta zo ta yi wa mutanen kasuwar jawabi kan mahimmancin zaman lafiya a tsakanin juna.

” Bayan kungiyar ta tafi sai wasu matasa suka far mana a cikin gidajen mu.”

Wani mazaunin kauyen mai suna Akilu ya ce sun sami mafaka ne a ofishin ‘yan sanda a ka kawo musu harin.

” Mun dauka cewa yadda jami’an tsaro suka yayyafa wa rikicin da aka yi ranar Litini ruwan sanyin komai ya wuce kenan amma sai gashi yau mune aka fatattaka daga gidajen mu haka kawai.”

Akilu ya ce sun dade suna zaman lafiya da yaruruka dabam-dabam a kauyen amma tun da haka ya faru bai tsamanin wani cikin su zai iya komawa da zama a wannan kauye.

Ya ce bayan gidaje da dukiyoyin mutane da aka kona babu wanda ya rasa ransa amma sai dai matasan da suka kai musu hari sun ji wa wani tsoho a kauyen rauni.

Share.

game da Author