RIKICIN APC A KADUNA: Kwamitin sasantawa ta fara aiki

0

Jam’iyyar APC ta kafa kwamiti domin sasanta bangarorin jam’iyyar dake fama da rikici a jihar Kaduna.

Gidan jaridar ‘PUNCH’ ta rawaito cewa kwamitin wanda ya hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti Segun Oni, Oditan jam’iyyar na kasa, George Moghalu da Rahmatu Alliyu sun fara aikin su ne a ranar Lahadi inda suka yi tattaki zuwa Kaduna domin tattaunawa da bangarorin jam’iyyar da kowa ya wasa wukar sa.

Gidan jaridar ta rawaito cewa kwamitin bata samu daman tattaunawa da bangaren sanata Hunkuyi ba saboda latti da Kwamitin tayi na isa Kaduna.

Ko da yake sun sami damar ganawa da shi Sanata Hunkuyi, a tattaunawar su Kwamitin sun roke shi da su hakura da juna su sasanta tsakanin su a Jihar.

Segun Oni ya bayyana cewa tun farko sun gana da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I da kuma mataimakin shugaban jam’iyyar na Yankin Arewa Maso Yamma Inuwa Abdulkadir.

Daga karshe Hunkuyi ya fadi wa kwamitin cewa lallai fa sai sun rufe idanuwar su idan suna so su sasanta wannan rikici. Su tsaya kan gaskiya da yin adalci.

Share.

game da Author