Rijiyoyin mai kayan gadon al’ummar Neja-Delta ne – Gwamna Dickson

0

Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya bayyana cewa ya kamata a kara bai wa ‘yan asalin yankin Neja-Delta rijiyoyin danyen man fetur, saboda dukiyoyin albarkatun kasa ne da suka gada tun kaka-da-kakanni.

Ya kuma yi kira ga kamfanonin kasashen Turai masu aikin hakar mai da su koma yankin Neja- Delta dungurugum, tunda daga can ne su ke hako danyen man fetur din.

Dickson ya yi wannan kalubale ne a ranar Asabar, lokacin da ya ke aza harsashen aikin kamfanin matatar mai na Aziken Petroleum Refinery, a Obunagha Gbarian, Yenagoa.

Cikin wadanda suka halarci bikin kaddamar da aza harsashin har da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

“Ya kamata mu rika zuba jari wajen mallakar rijiyoyin mai, tunda dama man nan dai na mu ne iyaye da kakanni. Shi ya sa a duk lokacin da na samu sarari zan jinjina wa shugaba Muhammadu Buhari, amma kuma zan ce masa, mu na bukatar kari, domin kari ba ya kin dadi.

“Ni dai ban ga adalci ba a ce ana ta gina ramuka ana kafa bututun mai ya na ratsa garuruwa da jihohi, amma kuma wai babu matatun mai a yankin da ake hako danyen man nan.

“Sannan kuma na tsaya tsaf na yi bincike da nazari. A dukkan kasashen duniya da ake hako danen mai, a kowace kasa kamfanonin da ke hakar man su na da hedikwata a yankunan da su ke hako man. Amma banda Najeriya.

“Domin haka muna jira mu ga an yi haka a Najeriya, tunda dai man nan da ake ta tinkaho da shi, kayan gadon mu ne iyaye da kakanni.

“Amma fa mu ba mu ce kada wasu su ci moriyar ba, amma idan wasu na cin wannan moriyar mu kuma da ke yankin aka hana mu amfana da kayan mu, to a nan kuskuren ya ke.’’ Inji Dickson.

Share.

game da Author