Wani Dan Majalisa Mohammed Usman ya koka kan yadda gwamnatin Najeriya ba ta ware isassun kudade don dakile yaduwar cutar daji a kasar nan.
Usman ya ce a sanadiyyar wannan sakaci cutar na ta yaduwa, inda bayanai ke nuna cewa akan rasa rayukan mutane akalla 10,000 duk shekara.
Ya kuma kara da cewa kamata yayi gwamnati ta na ware akalla kashi 15 bisa 100 na kasafin kudin ta kasa duk shekara domin inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan.
” Amma sai gashi yau an wayi gari kudaden da fannin kiwon lafiya ke samu a kasafin kasar nan baya isan ta yin komai.”
Ya ce idan fannin kiwon lafiya na fama da irin wadannan matsalolin dole ne cutuka su addabi mutanen kasa.
Discussion about this post