Hukumar NACA ta yi kira da kakkausar murya da ba masoya shawara da a kiyaye da saduwa da juna ba tare da kariya ba.
Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ne ya sanar na haka a wata takarda da ya sa wa hannu domin yi wa masoya gargadi game da ranar masoya.
Ya yi kira ga matasa da su nemi sanin matsayin su game da cutar kanjamau ganin cewa yanzu matasa ‘yan shekaru 15 zuwa 24 sun fi kamuwa da cutar a Najeriya.
” Ina kira ga masoya da su yi amfani da wannan rana na masoya don sanin matsayin su game da cutar Kanjamau. Kashi 17 bisa 100 ne kawai na matasa suka san matsayin su game da cutar Kanjamau, saboda haka ne ya zamo abin tsoro ga mutane da kowa ya shiga taitayin sa.
Ayi hattara, A raba soyayya ba Kanjamau ba.
Discussion about this post