Ranar wani barawo ta baci, a lokacin da aka damke shi, bayan ya saci makudan kudaden wani fasinja a cikin jirgi, a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Lagos.
Mutumin mai suna Kunle Oni, an damke shi ne a cikin jirgin sama na kamfanin Air Peace, mai lamba P47139 wanda ya isa Lagos daga Abuja a ranar Asabar.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an samu tulin kudi a cikin jakar mutumin, wadanda aka tabbatar da cewa daga cikin jakar wani fasinja ce ya farka ya kwashi kudin.
Jami’an ‘Yan sanda sun bayyana cewa katin shaidar wurin aikin da fasinjan da ya yi sata ya yi amfani da shi har ya shiga jirgi, na wani kamfani ne mai suna HB Company.
Sai dai kuma da aka kara tsananta bincike, an gano a cikin jakar sa ya na dauke da katin shaidar wurin da ya ke aiki masu yawa kuma na wurare daban-daban.
Da aka matsa masa lamba ya fadi lokacin da ya fara sata a cikin jirgin sama, sai Oni ya ce a cikin wannan shekarar ya fara.