Fitacciyar yar wasan fina-finan Hausa da Turanci, Rahama Sadau ta bi sahun jaruman duniya wajen nuna juyayin ta ga rasuwar shahararriyar jaruma Sridevi.
Sridevi ta rasu ne a Dubai, bayan ta halarci wani bukin aure.
Sridevi ta yi suna a harkar finai-finai ne tun bayan fitowa da tayi a wani babbar fim mai suna Mr. India.
Jaruma Rahama Sadau ta yi ta saka hotunan ta da bidiyo a shafinta na Instagram domin nuna juyayin kan rasuwar jarumar.
Daga cikin wadanda suka jajanta wa iyalan mamaciyar sun hada da firam ministan kasar Indiya, da jaruman duniya.