Patience Jonathan ta roki EFCC a janye karar ta, a sasanta a bayan fage

0

Uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan, ta nuna gajiya da shari’ar da ta ke yi da Hukumar EFCC, yanzu ta yi roko a janye kara domin a sasanta a wajen kotu.

A a ranar 30 Ga Janairu, 2018, lauyan Patience mai suna Ifedayo Adedipe, ya rubuta wasika a madadin ta, inda ta ke neman Hukumar EFCC ta janye karar da ta maka ta, a sasanta a wajen kotu.

Yanzu dai wasikar na hannun EFCC ta na nazarin ko dai ta karbi tayin da aka yi mata na janye kara, ko kuma a ci gaba da shari’a har sai Baba ta gani.

Lauyan ya kara da cewa ya na da yakinin cewa janye karar a sasanta a wajen kotu, shi ne mafi alfanu ga bangarorin biyu, na EFCC da kuma ita kanta Patience Jonathan.

“Mu na tabbatar wa EFCC cewa da gaske Patience ta yi har a cikin zuciyar ta, ba da wasa ko hila ba, don haka a shirye mu ke mu hada kai da ku. Da fatan za ku amince da wannan babban tayi da muka yi muku a cikin mutunci da girmamawa.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa Patience ta nemi a sasanta ne bayan da EFCC ta yi tuntube da wasu munanan bayanan yadda Patience ta rika jidar makudan daloli ta na kimshewa a bankin Sky Bank da First Bank, daga baya kuma ta rika kamfata ta na fita yin cefanen kece raini da kuma sayen tangama-tangaman gidaje da manyan rukunin unguwanni, wato estate-estate a cikin kasar nan.

A karshe dai da EFCC ta rika bin lunguna da kurden yadda aka rika karkatar da kudaden, an gano cewa miliyoyin daloli daga cikin su na da alaka da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Share.

game da Author