Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima na jihar Neja NYSC ta tallafa wa wasu guragu 10 da kekunan hawa a jihar.
Jami’ar hukumar Theresa Arokoyo ta sanar da haka a yau Talata a garin Minna inda ta kara da cewa sun zabo guragun ne daga kananan hukumonin dake karkashin hedikwatar hukumar da suka hada da Chachanga, Bosso, Paikoro, Lavun, Wushishi da karamar hukumar Shiroro.
Ta bayyana cewa hukumar NYSC ta yi hakan ne tare da hadin guiwar wata kungiya mai zaman kanta ‘Grace Project International’ domin samar wa gurargun sauki wajen gudanar da al’amurran su.
Discussion about this post