Nnamdi Kanu makaryaci ne -Gwamnan Abia

0

Kwanaki kadan bayan matar shugaban kungiyar taratsin kafa Biafra, Nmamdi Kanu, ta yi hira da BBC, har ta furta cewa yiwuwar zaben 2019 ya dogara ne ga bayyanar Nnamdi Kanu, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya bayyana cewa Nmamdi Kanu makaryaci ne, kuma munafiki ne.

“A duk lokacin da za ka yi magana da Nmamdi Kanu, maganar sa ta yau daban, ta gobe kuma daban, ba ya magana daya, kullum sai dawurwura ya ke yi.”

Haka gwamnan ya shaida wa sashen igbo na BBC, wanda aka bude kwanan nan.

An tura wannan hirar ta minti uku da ka yi da shi a shafin Youtube na gidan radiyon, a jiya Laraba.

“Sannan kuma ni bai taba tuntuba ba kafin ya dauki ko ma wane irin mataki ya dauka.”

“Gaskiya ana maida kabilar Igbo na-ware da gwamnati, amma ta yaya za mu iya kai inda mu ke fatan kaiwa ne? Wane ne zai iya jagorantar kabilar Igbo har mu cimma gacin da mu ke neman kaiwa? Mu na da isassun bindigogi ne idan har yaki ya barke?

Sannan kuma gwamnan ya ce abu mafi muhimmanci ma shi ne, kabilar Igbo ta fi sauran kabilun kasar nan so a zauna kasa daya a karkashin Najeriya.

Share.

game da Author