NHIS za ta maida hankali wajen yi wa jama’a aiki ne – Inji Yusuf Usman

0

Shugaban hukumar inshorar lafiya ta Kasa NHIS, Usman Yusuf ya bayyana cewa sama da kashi 90 bisa 100 na mutanen Najeriya basu cikin shirin inshorar lafiya.

Yusuf ya fadi haka ne a wani taro da ya halarta a Sokoto, inda ya kara da cewa lalle akwai aiki a gaban su idan suna so su cimma burin su na samar wa dukan dan Najeriya ingantaciyyar kiwon lafiya da ya kamace shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa wannan itace maganar da Yusuf ya yin na farko tun bayan dawo kan aikin sa.

Yusuf ya kuma yi kira ga mutane da su daina bari labaran da gidajen jaridu ke yadawa na dauke musu hankali, cewa da yawa labaran ba bu gaskiya a cikin su.

A karshe Yusuf ya ce baza suyi kasa-kasa ba wajen ganin sun sauke hakin jama’a da aka dora musu.

” Yaki da cin hanci da rashawa muke yi sannan ita ma kanta tana yaki da mu amma za mu ci gaba da yaki da ita domin dawo da darajar da muke da shi a idanuwar mutanen kasar nan.”

Share.

game da Author