NDLEA ta kama miyagun kwayoyin da ya kai Naira miliyan 31 a Kebbi

0

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA reshen jihar Kebbi ta kama masu siyar da miyagun kwayoyi shida tare da kilo garam 657.200 na miyagun kwayoyi a jihar.

Jami’in hukumar Suleiman Jadi ya sanar da haka wa kamfanin dillancin labaran Najeriya yau Alhamis a Birnin Kebbi.

Jadi ya ce sun sami nasarar hakan ne bayan samun bayyana daga mutane da kuma fakon masu siyar da miyagun kwayoyin da ma’aikatan su suka yi a jihar.

” Ma’aikatan mu sun dade suna fakon wadannan mutane sannan a cikin kwanaki biyu kachal muka sami nasaran kamasu.”

Ya ce a ranar farko sun kama kilo garam 421.100 na kwayar ‘Tramadol’, kg 30 na tabar wiwi, kg 198 na wata kwayar ‘Tramadol’ a karamar hukumar Dandi sannan a rana ta biyu sun kama wani shahararen mai siyar da miyagun kwayoyi da kg 8.00 na kwayoyin ‘Benhexol psychotropic da Diazapam’ a karamar hukumar Zuru.

” A lissafe kwayoyin da muka kama za su kai na Naira miliyan 31.”

Share.

game da Author