Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Kingsley Moghalu, ya bayyana cewa kasar nan ba ta da takamammen jami’an tsaro na ‘yan sanda, sai dai masu amsa sunan kawai.
Farfesa Moghalu ya bayyana haka a yau Litinin a wurin kaddamar da wani littafi mai suna BIG, a tsibirin Victoria Island, Legas.
Da ya ke magana a kan rashin tsaro a kasar nan, yayin da ya ke karantowa daga cikin littafin, Moghalu ya yi tsinkayen cewa ana tauye hakkin jami’an ‘yan sandan kasar nan, ba a biyan su abin da ya dace da daidai wahalar da suke yi, kuma kudin da ake kashewa wajen wadatar musu da kayan aiki bai taka kara ya karya ba.
Ya ci gaba da cewa, yayin da kasar nan ke bukatar karin jami’an ‘yan sanda, wadanda ake da su a yanzu ba su wuce dubu 350,000 ba, kuma yawancin su duk su na biye ne da manyan mutane su na gadin su.
Ya ce saboda an ki inganta aikin dan sanda ne shi ya sa aka wayi gari a kasar nan yanzu duk wata harkar matsalar tsaro, an kwaso sojoji an cusa a ciki.
Discussion about this post