NAHCON ta maida wa alhazan bara rarar kudin Hajji

0

Hukumar alhazai na kasa NAHCON ta mayar wa alhazan bara raran kudaden da suka da ya rage da ya kai Naira miliyan 820.

Hukumar NAHCON ta ce kowani alhaji zai karbi rarar raguwar kudin ne a ofishin hukumomin kula da walwalan mahajjata na jihar sa.

Kakakin NAHCON Adamu Abdullahi ya kudaden da za mayar wa alhazan sun hada da,

1. Wadanda basu sami damar zauwa aikin hajjin bara ba, kuma sun biya, wanda ya kama naira miliyan 181.

2. Rarar da aka samu na jigilan da ya kai naira miliyan 209.

3. Raguwar kudin abinci, wadanda ba a ba alhazai ba da kuma shima ya kai naira miliyan 46.1

4. Kudin runfuna da da naurorin sanyi da ya kai Naira miliyan 278

5. Sannan kuma da kudin ruwan Zam-Zam da ba a bada ba, naira miliyan 1.5.

Abdullahi ya kara da cewa hukumar ta fara biyan kudaden tun a watan Disambar 2017 sannan jihohi 11 sun fara karban kudaden su, sauran jihohi 13 za su karbi nasu ne a cikin wannan shekara.

Share.

game da Author