Kakakin jami’an tsaro na ‘Civil Defence Corps NSCDC’ Adamu Shehu ya ce wata mummunar hadarin mota ta auku a garin Majiya dake karamar hukumar Taura jihar Jigawa inda mutane 10 suka rasa rayukansu sannan 10 sun sami rauni.
Ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfani dillancin labaran Najeriya ranar Alhamis a Dutse.
Ya bayyana cewa inda hadarin ya faru da misalin karfe 11:30 na safiyar Alhamis amma ba a san dalilin faruwar hadarin ba.
” Hadarin ta auku ne tsakanin motar kiran Sharon da wata motar gidan radiyon Wazobia sannan wasu sun ce gudu ne da motar take shekawa ya yi sanadiyyar hadarin.”
Ya ce ma’aikatan su tare da wasu mutanen gari suka ceto wadanda suka sami raunuka sannana sun kai su asibitin Ringim.
Cikin mutane 10 da suka rasu akwai yara biyu, mace daya da maza bakwai sannan suma gawan su na asibitin Ringim