Hukumar kare hadurra na kasa FRSC ta ce tun da aka kafa ta ranar 18 ga watan Faburairun 1988 hukumar ta rage aukuwar hadurra a hanyoyin Najeriya da kashi 62 bisa 100.
Shugaban hukumar reshen jihar Kaduna Umar Ibrahim ya sanar da haka a taron cika shekaru 30 da kafa hukumar wanda aka yi a Kaduna.
” Binciken da muka yi ya nuna cewa daga shekarar 1988 zuwa 2016 aukuwar hadarra a hanyoyin Najeriya sun ragu daga 25,792 zuwa 9,694.”
Ibrahim yace sun sami nasarar haka ne saboda hubbasan da hukumar tayi wajen wayar da kan mutane game da bin dokokin hanya da yin tuki tare da kula.
Ya kuma yabawa ma’aikatan hukumar cewa lallai sun cancanci yabawa, sannan ya ce hukumar zata ci gaba da basu kwarin guiwa domin ganin hakan ya dore.
A karshe hukumar ta Karrama wasu ma’aikatan hukumar da ya hada da Waheed Salihu, Sani Gwom Ambisa, Aliyu Audu, Isah Kabir, Halilu Abubakar da Lawal Ahmed saboda da kwazon aiki da suke yi.
Discussion about this post