Kungiyar malaman Najeriya NUT reshen jihar Adamawa ta sanar cewa ta rasa malamai takwas a rikice-rikicen da aka yi ta fama dashi tsakanin makiyaya da manoma a jihar.
Shugaban kungiyar Rodney Nathan da ya tsokata wa manema labarai a Yola ya ce bayan rasa malamai takwas da suka yi da yawa sun rasa wuraren zaman su inda yanzu haka suna gudun hijra a wasu garuruwan.
” Wannan rikice-rikicen ya sa mun rasa shugaban makarantar firamare daya a Demsa, malamai uku a Numan, malamai uku a Song sannan da malami daya a Madagali.”
Rodney ya yaba wa gwamnan Jihar Jibirilla Bindow, da kokarin da yayke yi na ganin an kawo karshen wannan fitina.
Discussion about this post