Shugaban Tsara Dabarun Yakin Operation Lafiya Dole, Rogers Nicholas ya ce rundunar sojojin Najeriya sun kakkabe Boko Haram baki dayan su.
Manjo Janar Rogers ya bayyana haka ne yayin da ake kaddamar da rundunar hadin-guiwa tsakanin Najeriya da Kamaru a ranar Asabar.
Ya kara da cewa rundunar Operation DEEP PUNCH II ta mamaye kuma ta lalata babban sansanin da Boko Haram ke takama da shi a cikin Sambisa.
Ya ce a lokacin da aka mamaye wurin, daruruwan ‘yan Boko Haram sun yi saranda sosai. Yayin da wasu da dama suka tsere.
Ya kuma ce an ceto daruruwan wadanda aka yi garkuwa da su.
“Mun karya lagon Shekau kuma mun karya lagon rundunar maharan sa. Sansanin da ya ke takama da shi ma ya na hannun mu.”
“Mu na ce wa mayakan sa kowa ya yi saranda ko kuma su ji a jikin su.”
Daga nan sai ya yi kira ga wadanda aka yi garkuwa da su da ‘yan Boko Haram da ke boye a cikin jeji da su fito su bada kai, ba wanda zai kashe su.