Wasu daga cikin ministoci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sun fara nuna alamun son komawa jihohin su don yin takarar gwamna a 2019.
Wasu daga cikin su za su fafata ne da gwamnonin da ke kan kujerun mulki, wasu kuma za su goge raini ne da wadanda gwamnonin da za su sauka suka tsayar wato shafaffun su.
A wannan Nazari da PREMIUM TIME tayi, ta kawo muku ministocin da alamu duk sun nuna cewa za su fito takara a 2019, sannan a shirye suke da su ajiye aiyukan su domin haka.
ADEBAYO SHITTU- OYO
Adebayo Shittu, dan asalin jihar Oyo ne kuma shine ministan Sadarwa. Adebayo ne na farko cikin ministocin da ya nuna sha’awar sa na yin takarar gwamnan jihar sa a 2019.
Ya bayyanawa jaridar Tribune cewa yana ta shiri domin tunkara kalubalen da ke gaban sa. Ya ce yana da yakinin cewa shine zai zamo gwamnan jihar Oyo bayan Ajimobi ya kammala wa’adin mulkin sa a 2019.
Sai dai wani hanzari ba gudu, tabbas zai fuskanci adawa masu tsauri, domin ko a can baya ba inuwar su daya da gwamna mai ci ba domin basa ga maciji duk da suna jam’iyya daya. A haka kuma tabbas bashi bane dan lelen gwamna Ajimobi wanda kusanta da gwamnan ko zai yi tasiri a zabe mai zuwa. Sai dai iya ruwa fidda kai.
AISHA ALHASSAN – TARABA
Mace mai kama da Maza, Aisha Alhassan ba boyayya bace a siyasar Najeriya. A zaben 2015 ta taka rawar gani a jihar Taraba in da sai da aka sake zabe karo na biyu kafin aka kada ta a zaben gwamnan jihar.
Minista Mata, Aisha bata daina harin wannan kujera na gwamnan jihar ba. Ana ganin tana daga cikin ministocin da zasu nemi kujerun gwamnan jihohin su. Wasu daga cikin masu muamula da minista Aisha sun tsokata mana cewa lallai Aisha na da wannan shiri a 2019.
KAYODE FAYEMI – EKITI
Tsohon gwamna kuma Ministan Ma’adinai, Kayode Fayemi, ya dade da nuna son zai fito takarar gwamnan jihar Ekiti.
Fayemi ya sha kasa ne a wajen Ayo Fayose na jam’iyyar PDP bayan sun fafata a zaben gwamna da yake neman zarcewa karo na biyu.
Fayemi bai sami nasarar doke Fayose sannan kuma shima Fayose din daga wannan karon sai kauye.
Wani abin da ba zai yi wa Fayemi dadi ba shine ganin yadda wani hadimin shugaba Buhari Babafemi Ojudu shima ya nuna karara cewa zai yi takarar Kujerar gwamnan jihar.
SULEIMAN HASSAN – GOMBE
Minista Hassan Adamu ne ya canji Amina Muhammed bayan ta amshi wani aiki a majalisar dinkin duniya.
Duk da cewa za a fafata sosai Idan har ba canza shawara yayi ba, akwai burbudin sa a tare dashi.
A Jihar Gombe jam’iyyar APC ta rabu gida uku ne. Na farko dai akwai wadanda ‘ya’yan jam’iyyar CPC ne ada wanda Shi Suleiman ke ciki, Akwai kuma APC bangaren ANPP sannan akwai na wadanda suks canza sheka ne daga PDP zuwa APC bayan an kafata.
Yanzu dai kowa na daura banten sa, mai rabo Ka dauka.
IBE KACHIKWU – DELTA
Ministan Albarkatun Mai na daga cikin wadanda a ke ganin zasu nemi takarar kujerar gwamna a Jihar Delta.
Duk da cewa jam’iyyar PDP ce ke mulki a jihar, alamu duk sun nuna cewa Kachikwu zai nemi kujerar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC.
Idan dai ba matsala aka samu da zai iya cukuykuye Kachikwu ba, komai zai iya faruwa.
MANSUR DAN-ALI – ZAMFARA
Mansur Dan-Ali, ministan tsaro na daga cikin wadanda akayi kiyasin cewa za su maye gurbin gwamna Yari idan ya kammala wa’adin mulkin sa a 2019.
Sai dai har yanzu abin bai fito fili ba ko zai yi takarar gwamnan ko A’A, alamu sun nuna cewa lallai akwai wannan shiri.
Makusantan minista Dan-Ali sun shaida mana cewa lallai za a iya ganin haka idan lokaci yayi, sai dai kuma Shi gwamna Yari bai ce komai ba kan ko waye zai mara wa baya idan zai sauka daga Kujerar gwamna a 2019.
Kada kuma a manta cewa kama kafa da Yari ba a nemi na Yerima, fa akwai matsala.
Discussion about this post