MDCN ta yi wa sabbin likitoci rijista

0

Kungiyar likitocin hakora ta Najeriya MDCN ta yi wa sabbin dalibai likitoci 249 da suka kammala karatunsu a makarantun kasashen waje rajista.

An yi wa daliban rijista ne bayan sun ci jarabawar kwarewa da suka rubuta.

” A lissafe Najeriya na da kashi 35 bisa 100 na likitoci da kashi 60 bisa 100 na likitocin hakora wanda jimlar hakan ya kama kashi 35.7 bisa 100 na karin likitoci a Najeriya.”

Idan ba a manta ba bara irin wadannan dalibai sun rubuta wannan jarabawa inda mafi yawa daga cikin su ba su ci jarabawar su.

Hakan ya sa iyayen daliban suka kai karan kungiyar MDCN majalisan dattijai da kotu kan cewa wai da gangar kungiyar ta kada su a jarabawar.

Shi ko ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da ingancin makarantun da suke tura ‘ya’yan su a kasashen wajen domin rashin samun ingantaciyyar koyarwa na daya daga cikin dalilan da ya sa dalibai suka kasa cin jarabawa.

Share.

game da Author