Masari ya nuna fushin sa ga rashin fara shirin aikin Hajji ga Hukumar Alhazan jihar

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya nuna rashin jin dadin sa kan rashin fara shirin tafiya hajji da hukumar kula da jin dadin alhazan jihar ba ta yi har zuwa yanzu.

Masari ya fadi haka ne a Katsina da yake tattaunawa da shugaban hukumar Salisu Shinkafi a fadar gwamnati.

” Sanin kowa ne cewa kowace shekara ana yin wannan tafiya amma haka bashine zai sa ku mike ku fara aiyukan da ya kamata ku yi ba cikin lokaci sai bayan lokaci ya kure sa ku zo kuna ta fadi-tashi kuna ce ba ayi wannan ba, ba ayi wancan ba”.

” Irin haka da kuka saba yi na kawo mana matsala da dama a lokacin aikin hajji din.”

Masari ya kuma kara nuna fushin sa kan canza wurin kwanana mahajjata da hukumar ta yi.

” Gwamnati ta samar muku da duk abin da kuke bukata amma ku da ake jira ku naku aikin kun kasa.”

Shugaban hukumar, Shinkafi da yake tofa alabrkacin bakin sa a tattaunawan, ya bayyana cewa malaman addini za su fara yi wa maniyyata wa’azi da tunatar wa tu daga watanni uku kafin a fara tafiya aikin sannan hukumarsu za ta kafa kotu a kasar Saudi da Najeriya domin yanke wa masu aikata laifi hukunci.

Share.

game da Author