Malami ya lakada wa dalibar sa duka har sai da ta rasa ran ta a jihar Zamfara

0

Maitaimakin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Muhammad Abubakar ya shaida wa majalisar jihar cewa wani malamin makarantar Sankalawa dake karamar hukumar Bungundu ya yi sanadiyyar ran wata dalibar makarantar sa da ya lakadawa dukan tsiya har sai da ta rasa ran ta.

Abubakar ya sanar da haka ne a zauren majalisar ranar Laraba inda ya kara da cewa lalle ya kamata su dauki matakin gaske game da hakan ganin yadda wannan ba shine karo na farko ba da ya faru a jihar.

” A kwanakin baya haka muka sami labarin cewa wani mataimakin shugaban makarantar mata a Kwatarkwashi ya ji wa wata daliba rauni sanadiyyar horo mai tsanani da ya yi mata.”

” Idan aka ci gaba a haka hana ‘ya’yan mu karatun Boko zai yi.”

Abubakar ya yi kira ga majalisar da ta gaiyaci kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha na jihar ya zo ya bayyana matakan shawo kan wannan matsala da ake fama da shi a makarantun jihar.

A karshe majalisar ta nuna bacin ranta game da abin da ya faru sannan ta umurci kwamitinta na Ilimi da ta gaiyato kwamishinan ilimi ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani a kai.

Share.

game da Author