Makiyayar shanun da Kano za ta kafa za ta dauki shanu miliyan biyar

0

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa makiyayar shanu da ta ce za ta gina a Dajin Falgore, za ta iya daukar shanu sama da milyan biyar.

Kwamishinar Harkokin Noma, Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Kamfanin Dillancin Labarai yau Alhamis a Kano.

Gawuna ya kara da cewa makiyayar za ta kunshi makiyaya da dabbobin na su, wanda hakan zai kawar musu da kwadayin tafiya kiwo daga wannan jiha zuwa waccan.

Tun cikin shekarun 1940 ne Turawan mulkin mallaka su ka kafa Dajin Falgore, amma sai bayan 1960 ne aka kara inganta shi.

“Dama tun da farko an tsara wurin ne yadda za a gina kasuwanni, wuraren shakatawa, makarantu, mayanka ta zamani, wurin yawon bude-ido, masana’antu wadanda za su saukaka wa makiyaya samun damar yin harkokin kasuwancin su a muhallin da su ke zaune, ba tare da fuskantar cikar ba.

Ya ce tuni an gayyaci wani kamfanin tuntuba da zai yi nazarin yadda makiyayar za ta kasance. Idan ya kammala, za a mika wa Shugaba Muhammadu Buhari rahoton.

Yusuf ya ce daga nazarin da aka yi, aikin zai cinye dala miliyan 30.

Share.

game da Author