Makiyaya da manoma sun yi taron zaman lafiya a Jigawa

0

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta gudanar da taron kara jaddada zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a jihar. An gudanar da taron ne karkashin hadin guiwa da kananan hukumomi takwas da ke shiyyar Arewa maso gabacin jihar tare da Masarautar Hadeja.

Taron ya bayar da damar da kowa zai bayyana irin shawarwarin da ya kamata a bi domin a shawo kan rikice-rikicen makiyaya da manoma a jihar da kuma ynkin Arewa maso gabas.

An gudanar da taron a garin Kirikasamma, a harabar hedikwatar karamar hukumar a ranar Laraba, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Bala Senchi.

Cikin wadanda suka yi jawaban jan hankalin jama’a da kauce wa rikice-rikice, har da Mataimakain Gwamnan Jihar, Ibrahim Hassan Hadeja da kuma Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta jihar Jigawa, Wada Maija’a.

Share.

game da Author