Majalisar wakilai ta sake zama domin yin nazari kan kudirin hana mutane fita kasashen waje neman magani a asibitocin can.
Sergius Ogun wanda ya jagoranci mahawaran a zauren majalisar ta zauna ne domin samun madafa kan yawan kudaden da kasan ke rasawa sanandiyyar fitar da mutane ke yi zuwa kasashen waje.
” Najeriya kan rasa dala miliyan 500 duk shekara dalilin fita zuwa kasashen waje da mutane kan yi neman magani.
Ya ce inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan ne kawai mafita sannan idan har aka samu nasarar haka wasu ma daga kasashen kusa da mu za su rika zuwa don ganin likitoci.