Majalisar Dokokin Jihar Kwara ta sa dokar hana sayar da barasa, shan ta da kuma sarrafa ta a cikin birnin Ilorin, babban birnin jihar.
An sa wa dokar hannu ne biyo bayan rahoton da majalisar ta fitar jiya Laraba.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa a karkashin wannan doka, ba za a sake amince wa wani ya rika dafa giya ko ya kafa masana’antar hada ta ba. Kuma haram ne a sayar da ita ko a sha ta a cikin babban birnin jihar.
Duk wanda ya karya doka zai biya tarar naira dubu 100,000 ko kuma daukin wata shida, ko kuma a hada masa biyun duka.
Kakakin Majalisar Ali Ahmed ya umarci magatakardar majalisar ya tura wa gwamna kwafen dokokin domin ya kaddamar da ita ta fara aiki.