Majalisar Dinkin Duniya ta nuna tsananin bacin ran ta dangane da sace dalibai mata 110 da Boko Haram suka yi a makarantar sakandare ta Dapchi, da ke jihar Yobe.
Shugaban Majalisar ne Antonio Guterres ya bayyana haka a cikin wani jawabi da kakakin yada labaran sa, Stephane Dujarric ta fitar, inda ya yi Allah-wadai da sacewar da aka yi musu da kuma sakacin da ya haifar da sace su.
Ya ce hankalin sa ya yi matukar tashi kuma ya na cikin damuwa jin yadda aka kutsa har cikin makaranta aka sace daliban mata a ranar 19 Ga Fabrairu, 2018, kuma aka arce da su.
Daga nan sai ya yi kira a sake su da gaggawa ba tare da gindaya wasu sharudda ba. Ya kuma ja kunnen gwamnatin Najeriya cewa ta gaggauta kubutar da daliban tare da kamo maharan da suka sace su, a hukunta su.
A karshe ya kara jajjada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wajen tabbatar da cewa an shawo kan Boko Haram da sauran tashe-tashen hankula masu alaka da ta’addanci.
MAJALISAR TARAYYA TA KAFA KWAMITI
Majalisar Tarayya ta amince da kafa kwamitin mai karfi wanda zai bincike yadda aka yi sakacin da ya haifar da sace daliban sakandare ta Dapchi.
Gaba dayan majalisar sun amince da haka bayan da Honorabul Lawal ya bayan da kudirin neman a kafa kwamitin.
Majalisar ta ce za a binciki idan har gaskiya ne an janye sojoji mako daya kafin a kai harin da aka sace dabiban su 110, kamar yadda gwammantin tarayya ta tabbatar da adadin su.
A DAINA DORA WA JUNA LAIFI -Dogara
Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa bai ji dadin yadda hukumomin tsaro na sojoji da ‘yan sanda ke dora wa junan su laifin wanda ya yi sakacin da ya haifar da sace daliban Dapchi.
Dogara ya ce ya kamata jami’an tsaro su bada karfi wajen ceto daliban da kuma magance Boko Haram tare da kamo wadanda suka sace daliban.
Discussion about this post