Majalisar Dattawa ta ki amincewa da rahoton kwamitin ta na ‘Yan sanda

0

A yau Laraba ne majalisar dattawa ta ki amincewa da rahotan da kwamitin ‘yan sanda ta mika a gaban ta cewa ba za ta yi amfani da shawarwarin da kwamitin ta bada ba a ciki ba ganin cewa ba ta yi binciken ta kamar yadda majalisar ta umurce ta tayi ba.

Idan ba a manta ba majalisar ta umurci kwamitin ne ta zauna da sifeto janar din ‘yan sanda Ibrahim Idris yayi mata bayani kan farautar wadanda ake zargi da kashe wasu mazauna jihar Benuwai da ake zargi Fulani da aikatawa da sauron tashin-tsahina da ake samu a jihar.

Kamar yadda majalisar ta bayyana, ta ce rahoton bai kunshi bayanai daga gwamnan jihar ba, Samuel Ortom, wanda hakan ba zai iya sa a samu gamsasshiyar bayanai da za su iya amfani da su ba.

Share.

game da Author