Mahara sun harbe daliban jami’ar Nasarawa biyu

0

Rundunar ‘yan sandar jihar Nasarawa ta sanar cewa wasu dauke da bindiga da ba a san ko suwaye ba sun bindige wasu daliban jami’ar biyu.

Jami’in harka da jama’a na rundunar Kennedy Idirisu ne ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a Lafia.

Idirisu ya bayyana cewa sun sami rahotan wannan mummunar aiki ne daga bakin rajistaran jami’ar cewa ‘yan bindigan sun kai hari kauyen Mararaba –Akunza wanda mafi yawan mazaunan kauyen daliban jami’ar ne da misalin karfe 10:30 na dare ranar Talata.

” Shigan su ke da wuya kuwa sai suka bude wuta. Daya ya rasu nan take, dayan kuma ya rasu a asibitin ‘Dalhatu Araf’ dake Lafia.”

Kafin ‘yan sanda su iso wannan wuri, maharan sun gudu inda sai da suka hada da sace kayan wasu daga cikin daliban sannan kuma ‘yan sanda sun fantsama don kamo wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.”

Share.

game da Author