Madrid ta ladabtar da PSG da ci 3-1

0

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa takwaranta PSG da ci 3 da 1 wasan cin kofin zakarun nahiyar turai.

Shahararren dan wasan ta, Christiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a ragar PSG inda mai tsaron baya, Marcelo ya zura ta ukun.

Dan wasa Rabiot na PSG, ne ya zura kwallo a ragar Madrid.

Da yawa ba a dauka wasan za ta kaya haka ba, ganin cewa PSG ce ta fara zura kwallo a ragar Madrid sannan ganin cewa suna da shahararron ‘yan wasa kamar su Neymar, Mbape da sauran su.

Share.

game da Author