Kungiyoyin Ma’aikatan Kiwon Lafiya za su fara yajin aiki

0

Kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya na JOHESU da AHP sun ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 su biya musu bukatun su ko su fara yajin aiki.

Kungiyar ta ce idan ba a biya musu bukatun su ba za su fara yajin aiki da ga ranar 1 ga watan Maris.

Kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiyar wanda ya hada da ma’aikatan jinya,masu gwaji da masu bada magani sun bayyana cewa gwamnati ta yi alkawarin biyan bukatun su wanda ya hada da karin albashi kamar yadda aka yi wa likitocin kasar nan, inganta fannin kiwon lafiya da sauran su, amma har yanzu shiru kake ji kamar an ci shirwa.

Share.

game da Author