Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus, ya bayyana cewa sabuwar kungiyar siyasar da Obasanjo ya kafa kuma ake kokarin yi mata rajista, ba wata barazana ba ce ga PDP idan zaben 2019 ya zo.
Secondus, wanda aka ruwaito a jaridar Punch, ya yi maganar ne a garin Asaba, babban birnin jihar Delta a ranar Lahadi da ta gabata yayin wata liyafa da shugabannin jam’iyyar na jihar Delta su ka shirya.
Cikin wadanda su ka halarci walimar har da Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe da Okozie Ikpeazu na jihar Abia.
Secondus ya ci gaba da bayanin cewa ya na da yakinin yadda al’ummar Najeriya su ka dawo daga rakiyar gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma a shirye su ke da su yi fatali da jam’iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.
Daga nan sai ya sha alwashin cewa daga yanzu PDP ba za ta sake yin karfa-karfar fitar da dan takarar da ba shi ’yan jam’iyya ke so ya tsaya musu takara ba.
Discussion about this post