Kotun Duniya ta kammala binciken kisan ‘yan Shi’a, ta fara binciken kisan ‘yan IPOB

0

Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Duniya, ICC, ta kamo hanyar gurfanar da wadanda ke da hannu a kisan daruruwan mabiya Shi’a da aka kashe a Najeriya a cikin watan Disamba, 2015.

Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara ya bayyana cewa ya kammala binciken sa game da kisan tun a cikin watan Disamba, 2017.

Har ila yau kuma ofishin ya ce ya mika wa gwamnatin Najeriya kwafen binciken da ya yi, domin su yi masa bayani kan abin da za su iya cewa.

ICC ta ce mummunan harin da aka kai wa ‘yan kungiyar IMN, sojoji ne su ka kai musu harin, wanda dukkan kungiyoyin kare bil adama ta duniya su ka yi tir da wannan kai hari, ya saba da ka’ida ta ‘yancin dan Adam.

ICC dai ta damka kwafen biciken ta ga Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami.

IMN ta bayyana cewa ta rasa mabiya sama da 1,000 a ranar 12 da 14 Ga Disamba, 2015, a Zaria.

Wakilin Gwamnatin Jihar Kaduna ya shaida wa kwamitin bincike cewa sojoji sun ba su gawawwakin mutane 347, inda su kuma su ka rufe su a cikin kabari baki daya.

Sai dai kuma duk da wannan bayanai, rundunar sojojin Najeriya ta ce masu zanga-zanga mutane bakwai kawai ta kashe, kuma sun rufe hanya ne da nufin kashe Hafsan Hafsosjin Soja, Laftanar Janar Tukur Buratai.

Baya ga wannan, a yanzu kuma wannan kotu ta bayyana cewa ta fara binciken kisan da ake zargin sojoji sun yi wa ‘yan Kungiyar IPOB, masu rajin kafa kasar Biafra.

An yi zargin cewa su ma wadannan mambobi na IPOB, sun fuskanci muzgunawar jami’an tsaro tun daga cikin watan Oktoba, 2015, lokacin da aka cafke shugaban su Nnamdi Kanu a Legas.

Daga nan aka maida Kanu Abuja, inda aka rika gabatar da shi kotu, har zuwa cikin Satumba, 2017, lokacin da ya sulale, ba a kara jin duriyar sa ba, tun a wannan rana da sojoji su ka yi wa gidan sa dirar-mikiya, a Umuahia.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta ruwaito wani rahoton kisan wasu ‘yan kungiyar IPOB 120 a cikin 2018, ta kuma ruwaito yadda aka yi musu kabarin-bai-daya aka rufe su.

Masu bincike da kuma gabatar da kara na kotun ta ICC, sun bayyana cewa sun bi hanyoyi sahihai da dama wajen tattara bayanan su, ciki kuwa har da rahoton da Kwamitin Binciken Musabbabin Rikicin, wanda gwamnatin jihar Kaduna ta kafa.

Idan har Babban Mai Gabatar da Kara na Kotun Duniya ta ICC ya bayar da amincewar a fara gudanar da shari’ar, to wannan ne karo na farko da za a gurfanar da wani dan Najeriya bisa tuhuma kan laifin cin zarafin bil Adama a kotun da ke birnin Hague.

Sai dai wani mai sharhin harkokin kasashen duniya, mai suna Inkenna Nwaegbe, ya ce kammala binciken kisan da aka yi wa ‘yan Shi’a zai iya zama wata gagarimar nasara ga masu rajin kare hakkin jama’a. Amma a ta bakin sa, ya ce da wuya abin ya yi wani tasiri, idan aka dubi yadda gwamnati ta ke kallon zargin da ake mata.

Ya ce har yanzu gwamnatin Najeriya ta kasa kama ko mutum daya da laifin kisan ‘yan Shi’a ko kuma kisan da aka yi wa mabiya IPOB.

“Ku duba ku gani, ko a batun kisan da aka yi wa mabiya Shi’a. Duk da cewa kwamitin bincike ya kama wani Manjo Janar da laifi, gwamnati ba ta dauki wani kwakkwaran mataki a kan sa ba.”

“Har yanzu Manjo Janar Oyebade na cikin sojojin Najeriya, ba a cire shi ba, sai ma karin daukaka da ya ke samu.

Ya kuma nuna damuwar, “har yau babu wata diyya da aka biya mabiya Shi’a ko ‘yan kungiyar IPOB, ballantana ma a ce an dauko wata hanyar sasanta rikicin.

Maimakon haka, shugaban Shi’a har yanzu ya na kulle, duk kuwa da kotu ta ce a sake shi tun cikin 2016.”

Share.

game da Author