Kotu ta ce Majalisar Dattawa na da ‘yancin kin amincewa da Magu

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayyana cewa Majalisar Dattawa na da dama da ‘yancin kin amincewa da Shugaban Hukumar EFCC na riko, Ibrahim Magu.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne makonni biyu da suka gabata, amma PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayanan hukuncin da aka zartas a yau Alhamis.

Hukuncin, kamar yadda Mai Shari’a John Dantsoho ya tabbatar, ya zartas da cewa EFCC ta yi kuskure da ta ce babu ruwan Majalisar Dattawa da yin katsalandan a kan wanda Shugaban Kasa ya turo sunan sa don ya zama shugaban EFCC.

Tuni dai Fadar Shauagaban Kasa ta taba aikawa da sunan Magu har sau biyu, amma Majaisar Dattawa ta ki amincewa da sunan.

Ita kuma EFCC ta ce aikin Majalisar Dattawa kawai shi ne ta rattaba amincewa da Magu, ba ta tsaya ka-ce-na-ce ba.

Mai shari’a ya ce Majalisar Dattawa na da damar tsayawa tsayin daka ta ga cewa sai wanda ya cancanta ne Shugaban Kasa zai nada a kan wannan matsayin shugabancin EFCC.

Share.

game da Author