Kotu dake yankin Kuje da, Abuja, ta ba da belin wata mata mai suna Khadija Yahaya, da ta kama da laifin tsoma hannun ‘yar kishiya a cikin tafasasshen ruwa.
Hukumar NAPTIP ne ta maka Khadija Yahaya a kotu dake Bwari Abuja saboda kona hannun dan kishiyar ta da ta yi da tafasasshen ruwan zafi.
Hukumar NAPTIP ta bayyana cewa Khadija wacce ke auran wani Mallam Yahaya a matsayin matar sa ta biyu ta aikata haka ne a ranar 12 ga watan Disambar 2017 a gidan su dake hanyar Old block Industry kusa da cocin ECWA a unguwan Chukuku dake yankin Kuje, Abuja.
” A wannan rana ne Khadija mai shekaru 30 ta zuba wani sinadarin dake yi wa fatar jikin mutum illa a cikin tafasashen ruwa sannan ta tsoma hannayen dan kishiyar ta mai suna Abubakar Yahaya mai shekaru 2 a cikin wannan ruwa.”
Ko da yake Khadija ta musanta aikata haka alkalin kotun A.O Musa ya bada belinta kan Naira 500,000 tare da takardar shaida daya sannan ya daga sauraron karan zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu.
Discussion about this post