Ruwan Kogin Tamburawa da ke cikin jihar Kano ya ci ran wata dalibar jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, mai suna Zubaida Nuhu. Sai dai kuma ana zaton Zubaida ta fada ruwan ne da nufin kashe kan ta.
Dalibar ta na karatun digiri na biyu ne a fannin Harkar Albarkatun Ruwa, kuma ta na dab da fara koyarwa a fannin, amma sai aka tsinci gawar ta a Kogin Tamburawa, a ranar Asabar da ta gabata.
Wani mai dibar yashi mai suna Ibrahim Musa, ya bayyana cewa marigayiyar ta je Tamburawa, inda ta tambayi a nuna mata bangaren da ya fi ko’ina zurfi a cikin kogin.
Ya ce to wannan ne ganin da aka yi mata na karshe.
Kawun ta mai suna Tajuddeen Alhaji, ya ce ta bar gida ranar Asabar da nufin za ta je banki ta ciro kudin da za ta tafi Zaria.
“A wannan rana ta fita da misalin karfe 11 na safe, kuma ta shaida wa mahaifiyar ta cewa za ta fita ta je banki domin ta ciro kudin motar tafiya Zaria. Bayan ta fita sai ta aiko wa mahaifiyar ta da wayar ta da kuma jakar ta.
“To ni kuma mahaifiyar ta sai ta kira ni wajen karfe 4 na yamma ta ce min Zubaida fa ta bar gida da nufin zuwa ciro kudi a ATM, amma har yanzu fa ba ta dawo ba. Nan da na nan ni kuma sai na sanar wa ‘yan sanda da kuma gidajen radiyo.” Inji shi.
Wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya wallafa, wanda ke nazarin halayya da tunanin jama’a, ya nuna cewa daya daga cikin kowane dan Nijeriya biyar na fama da matsananciyar damuwa.