KIWON LAFIYA: Menene mafita ga ‘Yan Najeriya, matsalar shaye – shaye ne ko Jabun magani?

0

Sanin kowa ne cewa daya daga cikin matsalolin dake dawo da hannun agogo baya a fannin kiwon lafiyar kasar nan shine rashin isassun kudaden da za a raya fannin.

Rashin ware wa fannin kiwon lafiya isassun kudaden aiwatar da aiyukanta ya haifar da matsaloli da daman gaske da a kullum ci baya a ke samu ba gaba ba.

Irin wannan sakaci da gwamnati ke yi ya sa yau an wayi gari ma’aikatan kiwon lafiya wato likitoci da kwararrun ma’aikatan lafiya daga kasar nan na warewa zuwa kasashen duniya don neman aiki.

Wadanda suke aiki a kasar kuma a kullum fama suke da matsalolin rashin albashi, alawus-alawus, rashin kayan aiki, jabun magunguna da dai sauran su.

Wasu cutuka da ke ci wa mutanen Najeriya tuwa a kwarya sun hada da:

1. Cutar Zazzabin Lassa:

Zazzabin Lassa, Wannan cuta dai kamar wasa ya na neman ya addabi mutanen Najeriya. Duk da cewa an fi kamuwa da shi ne a jikin kwari da beraye. A kullum karin samin mutanen da ke kamuwa da cutar a keyi.

Alamomin kamuwa da cutar zazzabin Lassa sun hada ciwon kai, ciwon kirji, ciwon gabobin jiki da naman jiki, kasala a jiki wanda ke sa mutum yawan kwanciya, suma, zubar da jini ta hanci, baki, makogoro da kumburin fuska da suran su.

Bincike ya nuna cewa a duk lokacin da cutar ta bullo mutane da dama kan rasa rayukan su. Bana da cutar ta bullo ta yi ajalin mutane da dama sannan mutane 77 na dauke da ita.

A yanzu haka asibitin Irrua dake jihar Edo ce kawai ke da kayan gwajin wannan cutar.

Hakan barazana ce ga ‘yan Najeriya domin kuwa ana samun karin yaduwar cutar kuma karancin asibitin da zai kula da wadanda suka kamu da cutar na tada wa ‘yan Najeriya hankali.

2. Cutar Kanjamau:

Har hukumomi an kirkiro domin taimakawa wadanda suka kamu da cutar a Najeriya, Hukumar NACA ta kashe biliyoyin naira domin wayar wa mutane musamman matasa kai kan yadda za su kare kan su daga kamuwa da cutar.

Kungiyoyi masu zaman kansu da kwamitocin majalisar dinkin duniya duk suna kashe makudan kudi a kasar nan domin ganin an sami nasara wajen dakile yaduwar cutar, amma kamar jefa allura ne a cikin teku. Kullum kara lalacewa yake.

Ko da yake ana yawan shelar cewa an sami nasarorin a wannan yaki da akeyi, a gaskiya akwai sauran rina a kaba.

Bincike ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika dake da yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau.

A Najeriya bincike ya nuna cewa kashi 4.2 bisa 100 na mutanen kasar masu shekara 15 zuwa 24 sun fi kamuwa da cutar sannan mafi yawa daga cikin su basu ma san suna dauke da cutar ba. Hakan babbar abin tashin hankali ne a kasar nan.

Sannan kuma mutane ba su zuwa asibiti domin yin gwajin cutar, kuma wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ba sa shan magani kamar yadda ya kamata.

Babban abin da ake rasawa a kasar nan musamman wanda ya shafi cutar kanjamau shine wayar da kan mutane. Wasu har yanzu na cikin duhu. Ya ra mata sa da ke tasowa na bukatan a wayar musu da kai kan wannan cuta sannan anuna musu hanyoyin da ake kama cutar da hanyoyin da za a iya samun zaman lafiya.

4. Zazzabin Cizon Sauro da Typhoid:

Zazzabin cizon sauro itama kamar yadda ake kamuwa da cutar shawara haka ake kamuwa da ita.

Bincike ya nuna cewa yara kanana da mata masu ciki na yawan fama da cutar a Najeriya.

Babbar matsalar kasar nan shine rashin tsaftace muhalli da mutane basu damu da shi ba. Wayar wa Mutane kai da kafa dokoki domin tsaftace muhalli na daga cikin abubuwan da ake bukata domin kawo karshen wannan matsala da ake fama da shi.

Sannan gwamnati su taimaka wajen yi wa mutane feshin kwari da sauro a unguwanni. Hakan zai rage yadda ake yawan fama da wannan cuta.

6. Jabun magunguna da Shaye – Shayen Miyagun Kwayoyi:

Siyar da jabun magunguna babbar matsala ce da ya zama ruwan dare a kasar nan.

Jabun magunguna sun karade kasar nan kaf, sannan abin sai kara yaduwa ya ke yi, ga kuma matsalar shaye-shayen kwayoyi da akeyi ba maza ba mata ba.

A karshe dai abin da ya kamaci gwamnati shine tayi matukar maida hankali wajen fifita fannin kiwon lafiya a mutanen Najeriya.

Ta kara fadada shirin inshorar lafiya ga mutanen kasa sannan ta nema kara tsananta doka kan masu siyar da jabun magunguna da matsalar shaye – shaye ga matasa.

Share.

game da Author