Kisan da Jami’an tsaro suka yi wa wani magidanci a Kano da sunan dan Boko Haram ne, abin tashin Hankali – Imam Murtadha Muhammad Gusau

0

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UUN! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UUN!! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UUN!!!

YA KU ‘YAN UWA NA, SHUGABANNI NA, MASU GIRMA, MASU DARAJA, MASU ALBARKA.

YA KU BAYIN ALLAH MASU KAUNAR ADALCI, MASU ADAWA DA ZALUNCI, MASU SON ZAMAN LAFIYA A YANKIN MU NA AREWA.

A GASKIYA TSAKANI DA ALLAH A YAU SAFIYAR LITININ (MONDAY), 19/02/2018 NA SAMU KAI NA A CIKIN FIRGICI DA MUMMUNAN TASHIN HANKALI DA DAMUWA, BA DOMIN KOMAI BA SAI DOMIN IRIN HALIN DA KASAR MU KE CIKI A YAU. INDA AL’AMARIN HAR YA KAI MU GA JAMI’AN TSARO ZA SU KASHE MUTUMIN DA BAI JI BA BAI GANI BA HAR LAHIRA, A GABAN IYALAN SA, SUNA KALLO, SANNAN DAGA BAYA KUMA SU KAMA DAN SA, SUYI MASA SHARRI DA CEWA SHI DAN BOKO HARAM NE!

WALLAHI ALLAH NE SHAIDA, NAYI KUKA SOSAI A KAN WANNAN AL’AMARI, NA RIKICE MATUKA KUMA NA DIMAUTA.

DON ALLAH WACE IRIN KASA CE WANNAN MUKE RAYUWA A CIKIN TA? WALLAHI DUK WANDA YA SAURARI SASHEN HAUSA NA MURYAR AMURKA (VOA HAUSA), A YAU LITININ DA SAFEN NAN, IN DAI HAR SHI MAI IMANI NE, DOLE YAYI KUKA SABODA TAUSAYI, KUMA DOLE YA SHIGA DAMUWA.

YANZU AN JEFA IYALAN WANNAN BAWAN ALLAH DA AKA KASHE A KANO CIKIN MUMMUNAN DAMUWA. DOMIN SHINE YAKE NEMO MASU ABINDA ZA SU CI. YANZU JAMI’AN TSARON NIGERIA SUN JEFA SU CIKIN WANI MUMMUNAN YANAYI NA RASHIN TABBAS.

INA KUNGIYOYIN DA KE IKIRARIN KARE HAKKIN DAN ADAM SUKE? GA FA INDA ZA KU YI AIKI, KAR KU SA MUNAFUNCI A CIKIN AL’AMURAN KU.

INA KANAWA DA DUKKAN WANI DAN NIGERIA MAI NEMAN TABBATAR DA ZAMAN LAFIYA DA ADALCI A CIKIN AL’UMMAH? LOKACI FA YAYI, KUMA DUNIYA TA ZUBA MAKU IDO, ANA KALLON SHIN ZAKU BARI WANNAN ZALUNCIN YA WUCE BA TARE DA YIWA WADANNAN YARA ADALCI BA?

DA WANNAN KUMA NIKE AIKA SAKO MAI KARFI ZUWA GA TUN DAGA MAI GIRMA PRESIDENT MUHAMMADU BUHARI, HAR ZUWA GA NSA MUNGUNO, MINISTAN TSARON NIGERIA, ‘YAN MAJALISUN TARAYYA, MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI, MAI MARTABA SARKIN KANO DA DUKKAN SARAKUNAN MU MASU DARAJA, GWAMNATIN JAHAR KANO, IG OF POLICE, GENERAL BURUTAI, DG SSS, DA DUKKANIN MANYAN MU NA AREWA, DA SUYI KOKARIN GANIN AN DAUKI MATAKIN ADALCI AKAN WANNAN ZALUNCI DA AKA YI WA WADANNAN BAYIN ALLAH A KANO. JAMI’AN TSARO SUN KASHE MASU MAHAIFI SUNA KALLO, KUMA DUK WANNAN BAI ISA BA, KUMA ANA SO AYI MASU SHARRI WAI KANEN SU ABUBAKAR DAN BOKO HARAM NE. AN YA KUNA GANIN ZA’A SAMU ZAMAN LAFIYA DA CI GABA A INDA AKE TAFKA IRIN WANNAN ZALUNCI DA KAMA-KARYA? TA YAYA JAMI’AN TSARON DA HAKKIN SU NE SU TAIMAKI MARASA KARFI WAJEN KARE RAYUKAN SU DA DUKIYOYIN SU, AMMA SUKA BUGE DA ZALUNTAR AL’UMMAH? KADA MU MANTA FA CEWA, IRIN WANNAN ZALUNCIN NE FA YAKE HAIFAR DA MASU AKIDA IRIN TA BOKO HARAM DA AKIDAR TA’ADDANCI A CIKIN JAMA’AH FA?

DON ALLAH! DON ALLAH!! DON ALLAH!!! YA KU SHUGABANNIN MU, INA ROKON KU, A MATSAYINA NA MAI DA’A DA BIYAYYA A GARE KU, MAI YI MAKU KYAKKYAWAN ZATO NA ALKHAIRI HAR KULLUN KUMA HAR ABADA, DA KU TAIMAKA, KU TABBATA AN YI WA WADANNAN BAYIN ALLAH ADALCI. AYI BINCIKE A KAN WANNAN AL’AMARI, A HUKUNTA DUK WANI JAMI’IN TSARO DA KE DA HANNU WURIN WANNAN AIKA-AIKA.

MAI GIRMA GWAMNA ABDULLAHI UMAR GANDUJE, MAI MARTABA SARKI MAI ADALCI, MUHAMMADU SANUSI II, A JAHAR KU WANNAN ABU YA FARU, DON ALLAH INA ROKON A BINCIKA, AYI ADALCI, DOMIN KAUCEWA FARUWAR WANI ABU MARAR DADI.

NAGODE, NAGODE, NAGODE.

NAKU, MAI KAUNAR KU, MAI BIYAYYA A GARE KU HAR ABADA:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi +2348038289761

Share.

game da Author