Hanzarin yanke shawarar da kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC ya yi har ya kara wa mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar wa’adi, ya faru ne da nufin kauce wa kuskuren da jam’iyyar PDP ta tafka cikin 2013, wanda shi ne sanadiyyar barkewar jam’iyyar, kuma ya yi sanadiyyar faduwar ta zabe.
Wannan bayani ya zo daga bakin wasu manyan jami’ai na jam’iyya wadanda suka labarta wa PREMIUM TIMES haka.
An dai kara wa shugabannin jam’iyyar a fadin kasar nan na jihohi 36, Abuja da shugabannin jam’iyyar na kasa wa’adin ne a taron da APC ta gudanar jiya a hedikwatar jam’iyyar, a Abuja.
Cikin watan Yuni mai zuwa ne ya kamata wa’adin shugabannin zai kare, amma sai aka kara musu shekara daya, ta yadda wa’adin nasu zai kare wata daya bayan rantsar da sabuwar gwamnati a zaben 2019.
Kakakin yada labaran APC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa “dukkan masu rike da mukamai ko na jiha ne ko na tarayya, to za su ci gaba da rike mukamin su amma a matsayin shugabanni na riko, har nan da wata shekara daya mai zuwa. Kenan an kara musu wa’adin watanni 12 cur.”
Alamomin cewa za a kara wa shugabannin wa’adi sun fara nunawa ne tun a ranar Litinin a lokacin da shugabannin jam’iyyar na jihohi suka hadu a Abuja, kuma suka nemi a kara musu wa’adin shekaru biyu.
Sun nemi a kara musu wa’adin ne domin su shawo kan kalubalen da ke gaban su kasancewa ga zabe ya kusa.
Sai dai kuma wannan shawara da suka yanke, ta ci karo da ra’ayoyin wasu manyan ‘yan jam’iyya, musamman ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu ya sasanta dukkan bangarorin da ke rikici.
“Shi kuma Tinubu bai goyi bayan karin wa’adin ba, sai ma ya nemi a yi taron gangamin jam’iyya a sake zabe, domin komai ya saisaita sosai kasancewa zaben 2019 ya kusa.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Majiyar ta ci gaba da cewa da farko shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ra’ayin Tinubu na a yi taron gangamin sake zabe.
Alamomin cewa Buhari ya fi karkata a sake zabe sun fito ne a lokacin taron kwamitin amintattu da aka yi a fadar shugaban kasa, inda ya bayyana cewa, “tunda ga shi INEC ta bayyana ranar da za a yi zabe, ina kira da a gaggauta yin taro na kasa da na jiha har ma da na mazabu da kananan hukumomi domin a tabbatar an yi zabe kan ka’ida ba a yi dauki-dora ba.”
Wata majiya ta shaida cewa akasarin gwamnonin da aka zaba karkashin APC sun fi karkata a kan a kara wa shugabannin jam’iyya su Odigie Oyegun wa’adin zabe.
Gwamnonin na ganin cewa idan aka ce za a yi zabe, to za a iya haifar da sabbin matsalolin da watakila ma su fi wadanda jam’iyyar ke fama da su a yanzu.
Daga nan ne inji majiyar sai Buhari ya nemi Gwamnoni da Tinubu kowane ya dubi dalilai na hujjojin da bangarorin biyu suka bayar.
Jawabi da Buhari ya yi a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa shugaban ya canja ra’ayin sa ne ganin yadda maimakon a jawabin sa ya yi maganar taron gangamin jam’iyya, sai ya ambaci zaben fidda gwani tunda zabe na kasa ya matso.
KOYON DARASI
Idan ba a manta ba, PDP ta yi taron gangamin jam’iyya cikin watan Agusta, 2013, wanda daga rigingimun da suka faru a wurin ne tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya jagoranci wasu gwamnoni bakwai suka fice daga wurin taron suka kafa ‘Sabuwar PDP”, wadda daga bisani ta narke da sauran jam’iyyun adawa aka kafa APC, wadda ta kwace mulki a hannun PDP a zaben 2015.
DA SAURAN RINA A KABA
Jawabin kara wa shugabannin jam’iyya na kasa da na jiha da kananan hukumomi wa’adi ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello. Sai dai kuma a gefe daya, yayin da wasu ke kallon cewa karin wa’adin da aka yi musu ya kauce ka’ida.
Wani abin dubawa kuma shi ne yadda aka fara taron aka gama aka bar Bola Tinubu da aikin sasanta bangarori masu rigingimu da junan su.
Sai dai kuma karin wa’adin ya saukaka kunnowar sabbin fitintinu da ka iya tasowa.
Discussion about this post