Shugaban ma’aikatar aiyukkan noma na jihar Katsina KTARDA Ibrahim Shehu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta horas da matasa 10,000 kan aiyukan noma a wata shirin da ta tsara mai suna ‘Accelerated Agricultural Development Scheme AADS’.
Ya sanar da haka ne a taron kammala horas da masu yi wa kasa hidima sana’o’in hannu da aka yi a sansanin Wamakko ranar Juma’a.
Ya ce wannan shiri zai taimaka wajen kawar da talauci tsakanin matasa a kasar nan sannan da bunkasa aiyukan noma.
Shehu ya kara da cewa dalilin wannan shiri babban bankin Najeriya zai samar da tallafi, wato jari ga matasan sannan su kuma jihohi su wadatar da filaye domin wadanda suka sami horon su yi aiki a kai.
Matasa 1000 ne za su fara amfana da shirin a bana.
Discussion about this post