KATSINA: 10 Ga Fabrairu za a yi zaben cike-gurbin Dan majalisar Tarayya

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ranar 10 Ga Fabrairu ne za a gudanar da zaben raba-gardama a wasu mazabu 15 a kananan hukumomin Mashi da Dutsi.

Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Katsina, Alhaji Jibrin Zarewa ne ya bayyana haka a Katsina.

Jami’an INEC su 130 ne za su gudanar da zaben a rumfuna 9 cikin karamar hukumar Mashi, yayin da za su kuma gudananr a rumfuna 6 cikin karamar hukumar Dutsi.

Kotun sauraren kararrakin zabe ce ta ce a sake zabe a rumfunan, bayan da jam’iyyar PDP ta kai karar cewa an yi kwange a zaben, don haka su na ja da nasarar da aka ce Mansir Ali-Mashi na APC ya yi a kan dan takarar PDP, Nazifi Bello a zaben da ya gudana ranar 20 Ga Mayu, 2017.

Share.

game da Author