Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, mai kula da Shiyya ta 5, Rasheed Akintunde, ya bayyana cewa kashi biyu cikin 100 ne kadai na ‘yan sandan Najeriya ke aikin kare rayuka da dukiyoyin kasar nan.
“Sauran kashi 80 duk sun buge wajen gadin manyan mutane a kasar nan.”
Akintunde ya bayyana haka yau Alhamis a Hedikwatar ‘Yan sanda ta jihar Bayelsa a yayin da ya kai wata ziyara.
Ya nuna matsanancin haushin sa ganin yadda wasu mutanen da ke kiran kan su manya ke neman a ba su har jami’an tsaro kamar 30 domin su rika kare lafiyar su a duk inda su ka shiga.
Hakan ya ce ya na haifar da karancin jami’an tsaron da ake dora wa aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.
“Kowane mai kiran kan sa babba ya na neman cincirindon ’yan sanda domin su kare shi da iyalin sa, Maimakon ya taimaka wa ‘yan sanda su yi aikin kare al’umma baki daya.
“Mambobin Majalisar Tarayya kowa na neman a ba shi jami’an tsaro. Kai hatta fasto da Rabaran duk nema su ke ido rufe. Yanzu manya ke rike da kashi 80 sauran jama’ar kasa na rike da kashi 20 kacal kenan.
Daga nan sai ya hori jami’an tsaro da su rika aikin su tsakani da Allah da kuma cusa kishin kasa a zuci.
Kafin nan dama ya yi kira a sake fasalin tsarin aikin jami’an tsaro.