KARO-DA-GOMA: Sanata Adamu ya sha alwashin hana ‘yan majalisa tsageranci

0

Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka tsige daga matsayain sa na shugaban kungiyar sanatocin Arewa, ya sha alwashin hana duk wani tsageran dan majalisar dattawa da na tarayya yin rawar gaban hantsi.

Adamu, wanda jim kadan bayan tsige shi aka zarge shi da salwantar da kudin kungiya har naira miliyan 70, ya ce duk wasu mambobin APC masu goyon bayan makarkashiyar da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari, to ya fice daga APC din shi ya fi sauki a gare su.

Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar APC na jihar Nassarawa da suka kai masa ziyara a Keffi, ya ce masu yi wa Buhari makarkashiya, to su sani tamkar Najeriya ce su ke yi wa makarkashiya.

Jaridar THE NATION ta buga labarin ziyarar inda ta kara da ruwaito cewa, Adamu ya ce:

“Idan dan majalisa ba ya son jam’iyya, kuma ya na ji a jikin sa shi ba ma dan jam’iyyar ba ne, to ya fice mana. Ai shantale kafar Buhari, shantale kafar gwamnatin tarayya ne.

“Ba abin mamaki ba ne don dan PDP yaki mara wa Buhari baya. Amma ka na APC kuma ba ka son shugaban kasa ya yi nasara, to zaman me ka ke yi a cikin jam’iyyar? Ka fice ka ba mu wuri.”

“Kai ko da dan majalisa a PDP ya ke, akwai yanayin da zai kasance ba zai nuna siyasa ko bambancin ra’ayin jam’iyya ba, musamman dan majalisa wadanda su ne ke yi doka.”

Adamu ya ci gaba da cewa ai rashin kunya ce da rashin godiyar Allah, a zabi dan majalisa a karkashin jam’iyya, amma da wuyan sa ya fara kwari, ba zai yi wani abin a zo a gani ba, sai kwashe kafafun jam’iyyar da ta raine shi har ya zama wani abu a kasa.

Share.

game da Author