Shugaban Kamfanin BUA Group, Abdussamad Rabiu, ya bayyana cewa kamfanin sa zai gina babban asibi na zamani a Kano, wanda zai ci gadaje 220.
Asibitin dai za a kashe naira bilyan 7.5 wajen gina shi. Rabiu ya bayyana haka ne a lokacin da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya kai masa ziyara a ofishin sa da ke hedikwatar kamfanin a Lagos ranar Talata.
Za a gina asibitin ne a cikin tsakiyar birnin Kano, a karkashin Gidauniyar BUA.
Abdussamad ya kuma gode wa Gwamna Ganduje da ya bayar da fili a cikin Kano da za a gina wannan katafaren asibiti.
Ganduje ya gode wa kamfanin Bua sakamakon wannan kasaitaccen asibiti da zai gina, da kuma kamfanin casar shinkafa mafi girma a Najeriya da Bua ya kafa a Kano.